Dino Nema Yake Ya Hadiye Tabarya A Tsaye – Gwamna Bello

Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya kalubalanci Sanata Dino Melaye mai wakiltar mazabar majalisar dattawa ta Kogi ta Yamma cewar, don Allah ya kyale shi, domin ya fuskanci ayyukan da ke gabansa. Ya je ya fuskanci matsalar da ke tsakaninsa da ‘yansanda tunda nema yake ya hadiye tabarya a tsaye.

Bello ya furta hakan ne lokacin da yake bayani dangane da zargin da Sanata Dino Melaye yake yi ma sa, cewar yana aiki da ‘yansanda ne saboda ya bata ma sa, da yake karyata zargin da Dino Melaye yake, jami’in hulda da jama’a na gwamna, Kingsley Fanwo, ya wanke gwamnan daga duk wani zargi da ake yi ma sa na cewar, shi ne musabbabin halin da Sanata Dino Melaye ya shiga.

A cikin sanarwar da ya fitar Fanwo ya ce da ya yi kokari don ya gana da su’yansanda saboda shi ma ya ba da na sa bayanan a kan abin da duk ya sani dangane da zargin da ake yi ma sa. ‘’Shi gwamna mai bin doka da oda ne kuma dan Nijeriya ne, ba wanda zai so ya sa kansa cikin irin wannan matsala ba, ko a cikin gida ko kuma waje. Ba wata Hukuma da ta bayyana wani laifin gwamnan, saboda shi ya san mutuncin mutane, don haka ba ta yadda za a yi ya kawo masu raini.’’

‘’ Me kuma ya hada gwamnan da wannan al’amrin da , saboda ai su ‘yansandan ne suka kama wadanda ake zargi, saboda ai jam’an ‘yansanda ne suka kama su yaran, bayan haka kuma su wadanda ake zargi da aikata laifi, sune kuma suka bayyana wanda yake kawo masu makamai.

 

Babban abin da ya kamata ya ya yi shi ne ya wanke kansa, ya kuma bar zargin gwamna.

Ana cikin haka ne kuma sai ga majalisar dattawa ta kafa kwamitin da zai binciki zargi da Sanata Dino Melaye yake, kwamitin kuma shi ne na ’yansanda da shari’a, da kuma umarni na sa kwamitin ya kammala aikinsa cikin kwana biyu , daga nan kuma ya su bayyanawa majalisa abin da ake ciki, tsakanin al’amarin da ya shafi shi Sanata Dino Melaye da kuma Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Ana iya tunawa Sanata Dino Melaye tun bara, ya bayyanawa majalisar dattawa ana kokarin a kashe shi, ya kuma zargi Gwamnan jihar Kogi da kuma Taofik Isa.

Ranar 19 ga watan Maris ne rundunar ‘yansanda ta jihar Kogi ta kama wasu mutane biyu wadanda kuma ta gabatar da, wadanda kuma ta bayyanasu ‘yan barandar siyasa ne, da bindigogi biyu kirar AK47 sa kuma wasu bindigogi biyar da ake kira action machine, suka kuma yi bayanin Sanata Dino Melayen yake daukar nauyinsu.

Ranar 24 ga watan March sai ga shi Sanata Dino Melaye ya karyata maganar da su wadanda aka kama suka ce. Ya kuma bayyana cewar ba wadda ya kamata a kama bace, saboda ana son a kallafa ma sa abin da bai yi ba, a ce ya yi dole.

Ranar Laraba ta wannan mako da ya wuce ne shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya yi wani abu na ba zata , inda ya nuna rashin jin dadin sa, a kan yadda Sanata Dino Melaye a gaban majalisar dattawa. Kowa dai ya san shi Dino Melaye yana daga cikin ‘yan gaban shugaban majalisar dattawa, ko kuma a ce su ne ‘yan Mowarsa.

Saraki da yake fadin ta albarkacin bakisa inda ya yi bayanin dangane da wani sabon ci gaban da aka samu, inda wasu mutane biyu wadanda aka kama suka ce, shi ne ya ba su bindigogi da kuma kudi, maganar kuma da ake yanzu sun gudu, daga wurin da ‘yansanda suke tsare da su a Lokoja. Amma maimakon shi Dino ya ci gaba da bayanin abin da ya dame shi sosai, sai kuma ya koma da yin waka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here