Tashin Hankali: An Tsinci Gawar Ɗaya Daga Cikin Ɗaliban Islamiyya da Yan Bindiga Suka Sace a Neja

Win money on DrumbeatNews !!!

An gano gawar ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace a islamiyyar garin Tegina, jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa an tsinci gawar yaron ɗan shekara uku kacal a bayan garin Tegina.

Amma har yanzun, hukumar yan sandan jihar Neja bata ce komai game da tsintar gawar yaron da aka yi ba An gano gawar ɗaya daga cikin ɗaliban islamiyyar da yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, jihar Neja, kamar yadda the nation ta tabbatar.

Yaron ɗan shekara 3 yana daga cikin ɗalibai 156 da aka sace a islamiyyar Salihu Tanko dake Tegina.

An tsinci gawar ɗalibin ne a wani wuri mara nisa daga garin Tegina, amma har yanzun ba’a gano musabbabin mutuwarsa ba.

A halin yanzu, iyayen wasu daga cikin ɗaliban da aka sace mata guda biyu sun rasa rayuwarsu saboda takaicin abinda ya samu ‘yayansu. Tawagar iyayen ɗaliban sun nuna rashin jin daɗinsu kan yanayin yadda gwamnatin jihar take tafiyar da lamarin kuɓutar da ƴaƴansu.

Mako ɗaya da faruwar lamarin amma har yanzun babu wata tawagar gwamnatin jihar da taje garin domin jajanta musu. Iyayen yaran sun ce:

“Shugaban ƙaramar hukumar su, Ismaila Modibbo, shine kaɗai yake taimakawa wajen fafutukar haɗa kuɗin da yan bindigan suka nema, domin kuɓutar da ɗaliban.” Hukumar yan sandan jihar Neja bata fitar da rahoton gano gawar ɗaya daga cinin ɗaliban ba har yanzun da muke haɗa wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here