Bayan kwanaki da halaka Al-Barnawi, sojin Najeriya sun sheke magajinsa, Malam Bako

Win money on DrumbeatNews !!!

Dakarun sojin Najeriya sun sheke Malam Bako, shugaban ISWAP da ya gaji Abu Mus’ab Al-Barnawi.

NSA Munguno ya ce babu shakka sojin Najeriya sun nakasa ISWAP ganin cewa cikin wata 1 aka halaka shugabanninsu 2.

Munguno ya tabbatar da cewa yanzu haka kungiyar na fama da rikicin shugabanci, yarda, zargi da sauransu.

FCT, Abuja – Mai bada shawara ga shugaban kasa kan tsaron kasa, Babagana Munguno, ya sanar da kisan Malam Bako, shugaban ISWAP na yanzu wanda ya gaji Abu Mus’ab Al-Barnawi, TheCable ta wallafa.

Munguno, manjo janar mai ritaya, ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati kan ganawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da shugabannin tsaro a Abuja ranar Alhamis.

Kamfanin Dillancin Najeriya ya ruwaito cewa, shugaban ma’aikatan tsaro, CDS, Janar Lucky Irabor ya tabbatar da mutuwar Al-Barnawi a ranar 14 ga watan Oktoba.

Irabor ya ce: “Zan iya tabbatar muku da cewa Abu Mus’ab ya sheka lahira. Ya mutu kuma bashi da rai.”

A ranar Alhamis, NSA ya bayyana cewa magajin Al-Barnawi, Malam Bako ya sheka lahira tare da wasu jiga-jigan kungiyar ta’addancin, Daily Nigerian ta wallafa. Ya ce: “Bayanin cewa, dakarun sojin Najeriya sun yi aiki mai kyau saboda a cikin wata daya an hambarar da shugabancin ISWAP inda aka halaka Al-Barnawi.

“Kwanaki biyu da suka gabata, wanda ya gaje shi, Malam Bako, daya daga cikin fitaccen ‘yan majalisar Shura na kungiyar ya sheka lahira. “A halin yanzu suna fama da rikicin shugabanci.

Kun san wadannan abubuwan su kan zo da matsalolin yarda, fada, zargi da sauransu. “Toh gaskiya ayyukan dakarun sojin kasar nan a arewacin kasar nan ya matsantawa kungiyar Boko Haram da sauran ire-iren kungiyoyinsu na Sahara.”

Source: Naija News

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here