Labari cikin Hotuna: Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC a Aso Villa

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugaban kasa Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa (FEC) na mako-mako a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Hadimin shugaban, Buhari Sallau, shine ya bayyana haka a wani rubutu da ya fitar a dandalin sada zumunta tare da hotuna.

Majalisar zartarwan tarayyan Najeriya ta kunshi shugaban kasa, mataimakinsa, SGF, ministoci da sauran su.

Abuja – Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na can yana jagorantar taron majalisar zartarwa (FEC) a fadarsa dake Abuja, yau Laraba 24 ga watan Nuwamba.

Hadimin shugaban yace: “Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC, a gidan gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja, ranar 24 ga watan Nuwamba.”

Hadimin shugaban ya kuma tura hotunan yadda shugaban ke jagorantar taron tare da mambobin FEC da suka samu halartar taron na yau.

Mambobin majalisar FEC sun haɗa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, ministoci da kananan ministoci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here