Gwamnatin Katsina Ta Dauki Ma’aikatan Lafiya 1, 000 Aiki – Masari

Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnatin jihar Katsina ta dauki ma’aikatan lafiya 1, 000 aiki kari akan wadanda jihar take da su a wani yunkuri na bunkasa bangaren tattalin lafiyar al’ummar jiharsa.

Gwamnan Masari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Dutsi a yayin da yake kaddamar da shirin karbar haihuwa na makon kula da lafiyar yara.

Gwamnan ya ce; sun dauki wannan matakin ne da daukar sabbin ma’aikatan lafiyar domin ganin sun cike gurbin da ake da shi a bangaren a asibitocin gwamnati. Masari ya tabbatar da cewa; gwamnatinsa ta gyara tare da bunkasa wadansu asibitocin gwamnati.

 

A cewarsa kasafin kudin 2019, gwamnatin ta bai wa cibiyoyin kula da lafiya muhimmanci, inda za su bunkasa kowacce cibiyar lafiya guda a kowacce gunduma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here