Fadar Shugaban kasa bata fadi daidai ba game da ziyarar Buhari zuwa Amurka

Win money on DrumbeatNews !!!

 

Yanzu haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana Birnin Washington DC tun jiya inda zai gana da Shugaban kasar Amurkan Donald Trump a makon nan game da wasu muhimman batutuwan da su ka shafi manyan kasashen biyu.

Lokacin da fadar Shugaban kasa ta sanar da ziyarar ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya shi ne Shugaban kasar da zai fara ganawa da Donald Trump na Amurka daga Nahiyar Afrika tun da ya hau mulki.

Sai dai wani tsohon Hadimin Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi wa Fadar Shugaban kasan raddi inda yace karya ce kurum aka sharba da aka ce Shugaba Buhari ne wanda zai fara haduwa da Takwaran na sa Trump daga Kasar Afrika.

Reno Omokri a shafin sa na Tuwita yayi wa Jaridar Punch da ta dauki wannan labari gyara inda yace a shekarar bara Shugaban kasar Masar watau Abel Fatah Al-Sisi ya zanta da Donald Trump a Amurka don haka bai yiwuwa ace Buhari ne farko.

A baya dama kun ji cewa a baya Bashir Ahmad yace Shugaba Buhari ne wanda zai fara ganawa da Shugaba Trump daga cikin Shugabannin Afrika. Sai dai ba shakka wannan ne karon farko da Shugaban kasashen Bakar Fatar Afrika zai gana da Trump.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here