Donald Trump ya maka kamfanin Facebook da Twitter a kotu, ya bayyana dalili

Win money on DrumbeatNews !!!

Tsohon shugaban kasar Amurka ya maka kamfanonin Facebook, Twtter da Google kan dakatar dashi

Ya bayyana hakan a matsayin take hakkinsa na fadin albarkacin bakinsa a matsayinsa na dan Amurka

An dakatar da Donald Trump daga shafukan sada zumuntan a watan Janairu bayan wani hairgizi a Amurka.

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a ranar Laraba cewa yana shigar da kara a gaban kotu a kan Facebook, Twitter da Google, yana kara fadada ikrarinsa na ‘yancin fadin albarkacin baki da manyan kamfanonin fasahar suka dakile.

An dakatar da Trump daga shafin Twitter da Facebook bayan da wasu gungun magoya bayansa suka mamaye Capitol a wani mummunan hari a ranar 6 ga watan Janairu, inda kamfanonin suka nuna damuwar cewa zai karfafa tashin hankali a kasar, CBSNEWS ta ruwaito.

Trump ya bayyana cewa: “Muna neman a kawo karshen hana ruwa gudu, a dakatar da garkame bakinmu da kuma dakatar da bakanta sunayenmu, dakatarwa da sokewa da kuka sani sarai.”

“Ina da kwarin gwiwa cewa za mu cimma nasarar tarihi ga ‘yancin Amurkawa kuma a lokaci guda ‘yancin fadin albarkacin baki.”

Ya shaidawa manema labarai kamar yadda jaridar AFP ta ruwaito cewa: “A yau, tare da Cibiyar Nazarin Manufofin Amurka ta Farko, ina shigar da babbar kara a matsayin jagoran kan gaba, game da manyan kamfanonin fasahar da suka hada da Facebook, Google da Twitter da shugabanninsu, Mark Zuckerberg, Sundar Pichai da Jack Dorsey…” Manyan kamfanonin fasaha na kasar amurka sun zama “masu tilastawa ba bisa bin doka da oda ba,” in ji Donald Trump, wanda aka dakatar a shafin Facebook ranar 6 ga watan Janairun bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here