Da Duminsa: Fani-Kayode ya yi magana bayan da EFCC ta kama shi kan jabun takardu

Win money on DrumbeatNews !!!

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode ya ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ba ta kama shi ba.

Fani-Kayode ya ce ya mutunta gayyatar da EFCC ta yi masa sannan ya bar ofishin hukumar da ke Legas da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba.

Tsohon ministan wanda ya ce jami’an EFCC na da ladabi da kwarewa ya ce an bayar da belinsa ne saboda fahimtarsa.

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya musanta cewa hukumar EFCC ta kama shi.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kama Fani-Kayode a yammacin ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An ruwaito cewa an kama Fani-Kayode daga bisani aka kai shi ofishin hukumar ta EFCC na shiyyar Legas bisa zarginsa da yin magudi da kuma buga jabun takardu.

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa a baya an kama tsohon ministan da ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a watan Satumba.

Sai dai a shafinsa na Facebook, Fani-Kayode ya ce hukumar EFCC kawai ta gayyace shi ne, ba ta kama shi ba.

Rubutun ya karanta:

“Na isa otal din George don cin abincin dare, EFCC ba ta taba kama ni ba, an gayyace ni, na tafi zuwa Legas don ganawa dasu, na isa ofishinsu da karfe 2:00 na rana, na bar wurin da karfe 8:30 na dare. An ba da beli na saboda sani na. Sun kasance masu ladabi da kwarewa. Godiya ta tabbata ga Allah.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here