Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

Win money on DrumbeatNews !!!

Jami’an tsaro sun yi babban kama a jihar Imo bayan an yi ta kai hare-hare a sassan jihar a baya-bayan nan.

An kama wani mutum mai suna Nnamdi Okafor da ake zargin shine ya ke daukan nauyin kai hare-haren

– An yi ta kai wa ofishohin rundunar yan sanda hari ana tafka ta’adi a jihar ta Imo cikin yn kwanakin nan

Jami’an tsaro a jihar Imo sun kama wani da ake zargin shine ke daukan nauyin kai hare-hare a jihar, an kama shi ne a Aboha-Ohi kusa da Assembly Owerri/Orlu road.

Binciken da Vangaurd ta yi a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu ya nuna cewa sunan wanda ake zargin Nnamdi Okafor.

A cewar jaridar, Okafor wanda dan asalin garin Amanachi ne a karamar hukumar Orsu a jihar yana daya daga cikin wadanda ke daukan nauyin bata gari suna kai hare-hare.

An alakanta wanda ake zargin mai shekaru 42 da kashe-kashe, kona ofishin yan sanda da kai hari gidan gyaran hali a Owerri.

A wani rahoton da Sahara Reporters ta wallafa, an dade ana sa ido kan Okafor saboda zarginsa da alaka da hare-haren da bata gari ke kai wa.

Wata majiya da ta yi magana da jaridar ta bayyana cewa an kama Okafor, shugaban wani otel tun a watan Afrilu kan zarginsa da daukan nauyin yan daba da ke kai hare-hare a kudu maso gabas.

Kama Okafor na zuwa ne kwana daya bayan jami’an tsaro a jihar sun kama yan bindiga 12 da ba a san ko su wanene ba.

An alakanta wadanda ake zargin da hare-hare a ofishin yan sanda da gidan gyaran hali na Owerri.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here