An sanar da mataki na gaba a shirin N-Power na gwamnatin Buhari

Win money on DrumbeatNews !!!

Ma’aikatar Aikin jin kai ta kasa ta bayyana mataki na gaba a karkashin shirin N-Power da take dauka.

Ta ce tana shawartar wadanda aka zaba da su gaggauta hawa shafin hukumar don tabbatar da bayanansu.

Hakazalika an bada lambobin wayan da za a kira idan ma watakila an samu matsala wajen tabbatarwar Ma’aikatar Aikin Jin Kai da Ci Gaban Jama’a ta sanar da mataki na gaba ga masu neman shiga shirin N-Power karkashin Batch C Stream One.

Babban Sakatare, Bashir Alkali, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ya ce ma’aikatar ta fara mataki na gaba na yin rajista tare da tabbatar da adiresoshin imel ta masu neman shiga shirin.

Alkali ya yi kira ga wadanda aka zaba da su duba asusun sakonnin adiresoshin imail din su don tabbatarwa da samun karin bayani, The Nation ta ruwaito.

Ya kuma umarci masu neman shiga shirin da su shiga cikin shafin www.nasims.gov.ng don yin rajistar bayanan su tare da dangwalen yatsa. Hakazalika ya kuma shawarci masu neman karin bayani su tuntubi layin taimakon N-Power a 018888340 ko 018888189 ko kuma imel don tallafi a support.npower@nasims.gov.ng don amsa musu tambayoyinsu. Wannan shine karo na uku a daukar ma’aikatan wucin gadi a karkashin shirin na N-Power.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here