An samu jikkunan bakin haure 6 a gabar tekun Tunisiya

Win money on DrumbeatNews !!!

A gabar tekun kudu maso-gabashin Tunisiya an samu jikkunan wasu bakin haure 6.

An samu jikkunan bakin haure 6 a gabar tekun Tunisiya

A gabar tekun kudu maso-gabashin Tunisiya an samu jikkunan wasu bakin haure 6.

Bayanan da aka samu daga jami’an tsaro sun ce, a ranar Lahadi mutanen suka kama hanyar zuwa Turai bayan sun shiga jirgin ruwa a tsibirin Jerbe.

Jami’an tsaron sun ce, an samu jikkunan bakin haure 6 daga cikin su 10 da suka shiga jirgin ruwan.

An bayyana cewar mutanen su 10 ‘yan kasar Tunisiya ne da suka fito daga garuruwan Tatavin, Medenin da Gabes.

Bakin haure na yawan bi ta gabar tekun kudu maso-gabashin Tunisiya domin tafiya tsibirin Lampedusa na Italiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here