Al’ummar Bodo dake Najeriya na murnar samun nasara a kotu

Win money on DrumbeatNews !!!

Al’ummar Bodo dake yankin Naija Delta dake Najeriya sun bayyana farin cikin su da nasarar da suka ce sun samu cikin shari’ar da suke yi da kamfanin hakar man Shell da suke zargi da lalata musu muhalli.

 

Yayin yanke hukunci kan karar da al’ummar Bodo suka shigar a kotun dake London, mai shari’a Justice Cockerill tace ana iya cigaba da shari’ar ranar 1 ga watan Yulin shekara mai zuwa, sabanin bukatar kamfanin Shell na watsi da karar.

Mutanen Bodo sun shigar da karar ne inda suke bukatar kamfanin Shell ya tsaftace musu muhallin su da ya gurbata wajen aikin hakar mai sakamakon kwararar sa da aka samu.

A shekarar 2015 kamfanin Shell ya dauki alhakin aikata laifin, inda yayi alkawarin biyan dalla milyan 83 ga mazauna yankin da kuma tsaftace musu muhalli.

Tuni dai aka fara aikin tsaftace muhallin a karkashin gwamnatin Najeriya mai ci, amma mutanen Bodo na bukatar kotun ta sanya ido wajen tabbatar da cewar anyi aiki mai inganci wajen tsaftace musu muhallin.

Lauyan al’ummar Dan Leader ya bayyana farin cikin su da matsayin kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here