Akwai bukatar shugaba Buhari ya kafa cibiyar gyaran tunanin shugabanni masu cin hanci – Gwamna Bello

Buhari da Yahaya Bello
Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bukaci shugaba Buhari ya gina wata cibiyar saita tunanin masu cin hanci

Ya ce aikin cibiyar shine gyara da saita tunanin ‘yan siyasar dake assasa cin hanci da rashawa

Bello ya yi wannan kira ne yayin jawabi ga wasu magoya bayan jam’iyyar APC a Lokoja

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bukaci shugaba Buhari ya gina wata cibiya da za ta ke gyara da saita tunanin ‘yan siyasar dake assasa mummunar dabi’ar nan ta cin hanci da rashawa a Najeriya.

Bello ya yi wannan kira ne yayin gabatar da jawabi ga wasu magoya bayan jam’iyyar APC a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

KU KARANTA: Mafi rinjayen sanatocin arewa na tare da Obasanjo – Kungiyar sanatocin arewa

Da yake fadar illolin cin hanci, gwamna Bello, ya ce masu cin hanci da rashawa sun fi mayakan kungiyar Boko Haram illa.

Kazalika gwamnan ya zargi jam’iyyar PDP da dasa tsiron cin hanci da yanzu ya girma ya fitar da rassa ko ina cikin fadin Najeriya.

A cewar gwamnan, jagorancin shugaba Buhari ne kadai zai iya fitar da Najeriya daga kangin fatara da talauci.

A wani labarin mai alaka da wannan, shugabannin kasashen Afrika da su ka halarci taron kungiyar gamayyar kasashen Afrika da aka gudanar a kasar Ethiopia, sun zabi shugaba Buhari a matsayin jagoran yaki da cin hanci a kasashen Afrika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here