Zan Maida Abba Gida-Gida, Gida – Ganduje

Win money on DrumbeatNews !!!

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar PDP , Abba Kabir Yusuf, da magoya bayansa za su sha mamaki a zaben gwamna da za a sake gudanarwa a jihar.

Ganduje yace shi bai damu da tazarar da dan takarar PDP ya bashi ba duba ga abunda ya wakana a zaben da ba a kammala ba wanda ke cike da siyan kuri’u da kuma razana masu zabe da jam’iyyar adawar tayi.

Shugaban kwamitin yada labarai na APC a zaben 2019 Malam Muhammad Garba a wata sanarwa da ya saki a yau Talata, 12 ga watan Maris ya bayyan cewa APC da dan takarar za su ci gaba da samun nasara kamar yadda Kano za ta ci gaba da kasancewa jihar APC.

Yace yayinda Ganduje zai ci gaba da jajircewa ka gudanar da zabe na gaskiya da amana, an toshe duk wata kafa da ta basu damar yin magudi, siyan kuri’u da razana masu zabe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here