Zakzaky ya sauka Indiya lafiya – IMN

Win money on DrumbeatNews !!!
Zakzaky

Kungiyar IMN ta ‘yan Shi’a a Najeriya ta ce jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky ya isa kasar Indiya lafiya a ranar Talata, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter.

A ranar Litinin ne malamin addinin ya tafi kasar Indiya don neman magani kuma ya tashi ne daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kungiyar ta ce abin da ta dade tana gwagwarmaya ya tabbata, bayan fitar jagoranta nata neman magani zuwa Indiya.

Hakazalika kungiyar ta ce ta jingine duk wata zanga-zanga a yanzu saboda abin da ta dade tana gwagwarmaya akai ya tabbata.

Wakilin BBC Muktari Adamu Bawa wanda ya je filin jirgin saman Abuja ya ce jami’an tsaro sun ki ba shi damar ganin malamin addinin gabanin tafiyarsa Indiya.

Sai dai wani wakilin gidan talabijin na kasar wato NTA wanda shi aka ba shi damar zuwa wurin da Sheikh Zakzaky yake, ya ce ya hango lokacin da ake sanya shi a cikin jirgin saman kamfanin Fly Emirates bayan an kawo shi a keken marasa lafiya.

Hakazalika rahotanni sun ce malamin zai fara yada zango ne a birnin Dubai, kafin daga bisa ya wuce kasar Indiya, inda zai yi jinya a asibitin Medanta.

AHakkin mallakar hotoKUNGIYAR ‘YAN SHI’A TA IMN
Image captionSheikh Zakzaky tare da matarsa Zeenat lokacin da aka mayar da su Abuja daga Kaduna

Mun yi kokarin jin ta-bakin gwamnatin, amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba; har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Samuel Aruwan bai amsa kiran da muka yi ta yi masa a waya ba.

Akwai rahotannin da cewa a jiya Lahadi ne aka mayar da shi Abuja daga jihar Kaduna, inda yake tsare.

Wannan yana zuwa ne mako guda bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta ba malamin addinin damar zuwa kasar Indiya neman magani bayan gindaya masa wasu sharudda.

Bayan hakan ne kuma gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da bukata gaban babbar kotun jihar ta neman a sanya “wasu sharudda game da damar tafiya neman maganin” da kotun ta ba Zakzaky da mai dakinsa Zeenat.

Gwamnatin ta zayyano wasu sharudda bakwai ne da take so a cika gabanin tafiyar malamin addinin kasar waje.

Sai dai lauyan mutanen biyu Barrister Haruna Garba Magashi ya shaida wa BBC cewa za su kalubalanci matakin gwamnatin, yana mai cewa “ta yi ne domin kawo tsaiko kan tafiyar malamin neman magani”.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin kasar take rike da malamin addinin bayan wani rikici da mambobin kungiyarsa suka yi da sojoji a garin Zariya na jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here