Zaftarewar kasa a Nepal

Win money on DrumbeatNews !!!

Mutane 8 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a Kasar Nepal.

 

Zaftarewar kasa a Nepal

Mutane 8 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a Kasar Nepal.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, an samu zaftarewar kasa a garin Bhaktapur sakamakon mamakon ruwan sama.

Kakakin ‘yan sandan Bhaktapur Himal Shrestha ya ce, an kubutar da mutane 111inda aka kwashe wasu sama da dubu 3 daga gidjensu.

An bayyana akwai mtane kusan dubu 1 da ke aikin ceto.

Sanararwar da Hukumar Kula da Yanayi ta fitar ta ce, za a ci gaba da samun ruwan saman a kwanaki masu zuwa.

A tsakanin watannin Yuli da Oktoban kowacce shekara ana samun mamakon ruwan sama a Nepal wanda ke janyo asarar daruruwan rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here