Zabtarewar kasa a mahakar zinare ta yi sanadiyar rayuka a Chadi

Win money on DrumbeatNews !!!

An bayyana cewar mutane 30 ne suka rasa rayukamnsu sanadiyyar zabtarewar kasa a filin da ake hakkar zinare a kasar Chadi.

 

An bayyana cewar mutane 30 ne suka rasa rayukamnsu sanadiyyar zabtarewar kasa a filin da ake hakkar zinare a kasar Chadi.

Yankin da ake hakkar zinarin mai suna Tibesti dake kusa da kasar Libiya ta zabtare ne lamarin da ya haifar da mutuwar mutane da dama kuma ana hasashen cewa kasa ta taushe al’umma da dama kamar yadda ministan tsaron kasar Mahamat Sala ya shaidawa kafar yada labaran Reuters.

Wani jam’in soja da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa kimanin mutane 30 sun hallaka.

Haka kuma wani dan majalisa a yankin ya bayyana cewa mutane da dama sun rasa rayukansu dangane da wadanda lamarin ya faru akan idonsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here