ZABEN 2019: Yadda Gaskiyar INEC Ke Kara Fitowa Fili

Win money on DrumbeatNews !!!

Kai tsaye ina so na fara da tunatar da masu karatu irin kokarin da INEC ta yi, inda ta shafe shekaru biyu ta na nanata wa jama’a ka’idojin da ya kamata a kiyaye da kuma dokoki kafin zabe da kuma lokacin zabe.

Amma abin takaici, daga cikin wasu muhimman dokoki 30, ‘yan siyasa da magoya bayan su sai da suka karya kusan 28.

YADDA INEC TA YI ADALCI
Kun tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha kaye a zaben Sanata a Rumfar Zaben sa?

Kun tuna INEC ta hana jam’iyyar APC shiga zabe tun farko a Jihar Katsina?

Kun tuna INEC ta bi umarnin kotu ta hana APC shiga zabe a Jihar Rivers?

Kun tuna yadda ‘yan jagaliyar siyasa suka rika banka wa ofisoshin INEC wuta a fadin kasar nan?

Zaben ‘inconclusive’ da aka rika kuka a kan sa, a jihohi shida dai duk jam’iyyar adawa ce ta yi nasara. Wato Adamawa, Bauchi, Sokoto, Benue, Taraba da Rivers.

Shin INEC ba ta nuna bacin rai dangane da rawar da jami’an tsaro suka taka a wasu wurare, musamman a Jihar Rivers ba?

Shin ba a yi wa INEC makarkashiya ba ne wajen kai hare-haren lalata kayan zabe?

Shin ba a rika bi ana banka wa ofisoshin INEC wuta ba, ana kone kayan zabe?

Shin INEC ba ta yi gargadin kada a yi wadannan laifukan ba ne?

WASU DOKOKIN ZABE DA AKA KARYA A 2019

1. Wanda ya yi rajista sau biyu.

2. Sojan-gona, wato yi wa ni rajista, ko yin rajista da sunan wani.

3. Tada hargitsi a lokacin kamfen.

4. Bayyana sakamakon zabe na bogi.

5. Kamfen a ranar zabe.

6. Saye ko sayar da kuri’a ko katin zabe.

7. Neman yin zabe a madadin wani.

8. Jefa kuri’a fiye da sau daya.

9. Hargitsa wurin da ake gudanar da jefa kuri’a.

10. Hana masu zabe yin zabe.

11. Fizgen akwatin zabe ko kayan zabe.

12. Lalata kayan zabe.

13. Aringizon kuri’u da rinton adadin kuri’un da aka jefa.

14. Cin zarafin jami’an zabe ko wasu masu ruwa-da-tsaki a harkar zabe.

15. Hana masu zabe hakkin su.

16. Lalata kayan zabe don kada a yi amfani da su wajen kafa hujja a kotun daukaka karar sakamakon zabe.

Saboda haka, jama’a da dama sun yarda da cewa, babu laifin INEC a yawancin wuraren da aka samu matsaloli a lokacin zabe ko lokacin kidayar kuri’u.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here