Yara dalibai na yawan kashe kansu a Japan

Win money on DrumbeatNews !!!

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewar yawan kashe kai da yara ‘yan makaramtun Firamare da Sakandire suke yi ya yi yawa a Japan wanda a cikin shekaru 32 da suka wuce abin ya fi tsamari a yanzu.

Yara dalibai na yawan kashe kansu a Japan

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewar yawan kashe kai da yara ‘yan makaramtun Firamare da Sakandire suke yi ya yi yawa a Japan wanda a cikin shekaru 32 da suka wuce abin ya fi tsamari a yanzu.

Mahukuntasun ce, wasu daliban na kashe kawunansu saboda takura daga iyaye ko makaranta ko kuma zalunci daga ‘Yan uwansu dalibai.

Alkaluman da aka fitar a hukumance na cewa, ya zuwa watan Maris din shekarar karatu ta 2016/2017 yara kana da ke makarantun Firamare da Sakandire 250 ne suka kashe kawunansu.

Wannan adadin ne mafi yawa a kasar tun bayan na shekarar 1986 da aka samu inda yara kanana 268 suka kashe kawunansu.

Sakamakon yadda yara 140 suka kashe kansu ba tare da barin wani rubutu ba ya sanya ba a san musabbabin daukar danyen matakin ba.

Jami’an Ma’aikatar Ilimi ta Japan Noriaki Kitazaki ya bayyanawa manema labarai cewar yadda daliban ke kashe kansu abun damuwa ne, akwa bukatar daukar matakan magance wannan lamari.

Ya ce, a shekaru 15 da suka gabata an samu saukin kashe kai daga ‘yan kasar Japan amma kuma har yanzu adadin yara kanana dake daukar wannan mataki na kara yawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here