Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

Win money on DrumbeatNews !!!

Dan majalisa dake wakiltan mazabar Obudu a majalisar jihar Cross River, Mista Steven Ukpukpen, ya fadi ya mutu a yayin motsa jiki da safiyar ranar Laraba

 

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:00 na safe a hanyar Moore dake Calabar. An rahoto cewa anyi gaggawan kai dan majalisan wani asibitin sojin ruwa dake kusa, amma likitan dake kan aiki yace yana cikin mawuyacin hali don haka ya tura su wani asibiti. Likitocin wani asibitin kudi da aka kai shi ne suka tabbatar da mutuwarsa. Sannan kuma asibitin koyarwa na jami’ar alabar ma da aka kai shi daga baya sun tabbatar da cewa ya mutu.

Da yakemartani kan lamarin, kakakin majalisar, Mista Gaul-Lebo yace yana cikin alhini kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here