‘Yan takarar neman shugabancin jam’iyyar PDP sai janyewa suke yi daya bayan daya

Win money on DrumbeatNews !!!

Ya zuwa yanzu ‘yan takarar neman shugabancin jam’iyyar PDP mutum uku ne suka bayyana janyewa daga takarar da suke yi. Mutanen sun hada da; Olabode George, Jimi Agbaje, da kuma Rashidi Ladoja.

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya bayyana janyewa daga takarar neman shugabancin jam’iyyar PDP.

A wani jawabi da ya fitar a yau Asabar, yayin da taron gangamin jam’iyyar ke gudana, Ladoja ya yi kira ga ragowar ‘yan takarar da su janye su bar wa tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran.

Olabode George

Ladoja ya ce “Mu bakwai ne daga yankin kudu maso yamma dake neman kujerar shugabancin jam’iyyar, kuma dukkan mu jam’iyyar ta tantance mu, amma ma su ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar sun nuna damuwar su da yawan ‘yan takarar daga yanki guda kuma sun bamu shawarar da mu rage adadin mu ya zuwa mutum guda, a son samu. Masu ruwa da tsaki daga arewacin Najeriya sun tabbatar mana cewar zasu zabi dan takarar yankin mu matukar muka fitar da mutum daya”.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayar da Lasisi ga sababbin jami’o’i 6

Ladoja ya kara da cewa “Na janye ne domin kishin yankin dana fito da kuma tabbatar wa da abokan mu daga arewacin Najeriya cewar a shirye nake na jingine bukatar kai na domin cigaban jam’iyyar PDP”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here