Rahotanni sun nuna cewa an kama wasu ‘yan ta’addar PKK guda 7 a kasar Nowe.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wasu ‘yan ta’addar PKK guda 7 a kasar Nowe.
Al’amarin dai ya faru ne a lokacin da ‘Yan PKK suka kai wa wasu Turkawa hari yayinda suke zaune a gidan shan shayi.
Ofishin ‘Yan Sandan birnin Oslo ya bayyana cewa mutanen 7 ‘yan ta’addan PKK ne sannan za a yanke musu hukuncin da ya kamata.
A gefe guda wasu ‘yan PKK kimanin 70 sun haifar da rigima a wani filin jirgin sama da Suwidin inda suka so su kai wa Turkawa farmaki.