‘Yan Najeriya ba zasu taba yiwa PDP afuwa ba – Jam’iyyar APC

Win money on DrumbeatNews !!!

– Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta mayar da martani ga kalaman afuwa da Ciyaman din PDP Uche Secondus ya furta

– Mataimakin Ciyaman din APC na Kano, Shehu Maigari ya ce babu wani dan Najeriya wanda ya san ya kamata da zai yafewa PDP abubuwan da tayi

– Maigari ya tabbatar wa yan Najeriya cewa tsarin da APC ta dauka na yaki da rashawa ta ta’addanci zaiyi nasara

Jam’iyya mai mulki ta APC reshen jihar Kano ta ce babu yadda za’ayi al’umman Najeriya su yafe wa jam’iyyar PDP irin ta’assar da suka kwashe shekaru 16 suna yi a kan mulki.

A yayin da ya ke mayar da martani kan rokon afuwa da shugaban PDP, Prince Uche Secondus ya yi ga yan Najeriya, Mataimakin Ciyaman din jam’iyyar APC na Jihar Kano, Honarabul Shehu Maigari ya ce rokon na PDP abin dariya ne.

‘Yan Najeriya ba za su taba yafe wa PDP ba – Jam’iyyar APC Maigari ya kara da cewa, ya kamata Ciyaman din PDP ya sani cewa yan Najeriya ba sakarkaru bane da zasu yarda jam’iyyar da ta lalata musu tattalin arzikin kasa cikin shekaru 16 da suka wuce ta dawo ta rude su.

KU KARANTA: An damke dan Najeriya da miyagun kwayoyi na N800,000 a kasar Indiya Yayi karin bayani inda ya ce ‘yan Najeriya ba za su taba manta dimbin dalolin da gwamnatin PDP tayi wadaka da su ba tun daga shekarar 1999-2015 da sunnan gyaran wutar lantarki.

Ya kuma ce PDP tayi watsi da fanin noma wanda shine abin da gwamnatin PDP tayi ikirarin cewa yafi komi mahimmanci, ya kuma kara da cewa yan Najeriya ba za su manta da dimbin kudaden da aka karkatar ba da sunan siyo makamai don yaki da Boko Haram.

Babu wani dan Najeriya na gari da zai iya mantawa da kuma yafe wa PDP irin kurakuren da tayi,” Inji Maigari.

Ya kuma tabbatar da wa yan Najeriya cewa tsarin da gwamnatin APC mai ci yanzu ta dako wajen magance matsalolin tsaro da kuma cin hanci da rashawa da ta gada daga jam’iyyar PDP za su Najeriya ga cin nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here