‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a Mali

Win money on DrumbeatNews !!!

Mutane 7 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai wa shingen binciken ababan hawa na soji dake kudancin Mali.

 

'Yan bindiga sun kashe mutane 7 a Mali

Mutane 7 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai wa shingen binciken ababan hawa na soji dake kudancin Mali.

Kamfanin dillancin labarai na Mali Amap ya bayyana cewar wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin kan shingen binciken ababan hawa na soji a Koury dake garin Sikasso na yankin Yorosso.

An kashe jami’an jandarma 2, jami’in hana fasa kauri 1 da fararen hula 4 a harin.

Bayan kaiğ harin dakarun Mali sun je yankin da lamarin ya faru don hana afkuwr makamancinsa.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Tun shekarar 2012 aka fara samun arangama tsakanin ‘yan ta’adda da jami’an tsaro a yankunan tsakiya da arewacin Mali.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya (MINUSMA) mai sojoji dubu 15 da aka samar a 2013 tare da sojojin Faransa dake kai hare-haren Berkhane tun 2014 sun gaza samar da zaman lafiya a Mali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here