Yadda Sojojin Najeriya suka ceto wata tsohuwa da jikar ta daga Boko Haram

Win money on DrumbeatNews !!!

Dakarun Rundunar Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole da ke Jihar Borno, sun tseratar da wata dattijiya da jikarta daga hannun mayakan ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Mai magana da yawun Hukumar Sojin Kasa, Rundunar ‘7 Division’, Kwanel Kingsley Samuel, ne ya bayyar da wannan sanarwan a jiya.

KU KARANTA: Babban magana! Sojojin karya sun yiwa sojan gaske fashin motar sa ta hawa

Ya bayyana cewar Rundunar Sojojin sun tseratar da dattijiyar da jikarta ne a wani maboya da ‘yan ta’addan suka aijye su a dajin ta Sambisa.

Ya kuma ce ba za suyi kasa a gwiwa wajen gudanar da ayyukan su har sai sun tseratar da dukkan wadanda ‘yan ta’addan su ka sace, a ko ina su ke.

Sai dai kuma ya jawo hankalin jama’a da su yi waras da idanun su a kan wani motsi ko mutumin da ba su aminta da shi ba, su kuma sanar da jami’an tsaro game da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here