Yadda ake vegetable couscous

Win money on DrumbeatNews !!!

 

Abubuwan hadawa

 

 • Couscous
 • Butter (a narka)
 • Dafaffafen kayan ciki
 • Carrot (a yanka dogo dogo)
 • Tarugu (a jajjaga)
 • Albasa (ki yanka)
 • Ganyen Ugu ko Alaiyaho (ki yanka manya)
 • Dafaffafen kwai (ki yanka kanana)
 • Maggi
 • Man gyada
 • Gishiri kadan
 • Kayan kamshi
 • Foil paper

 

Yadda ake hadawa

 

 1. Ki dauko couscous na ki ki zuba mishi butter ko man gyada ki juya sosai har sai butter ya hade jikin couscous ajiye a gefe.
 2. Daura tukunya akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki kawo kayan ciki ki zuba, sai ki dauko tarugu ki sa ki juya ki soya sama sama shima.
 3. Sai ki dauko ruwan zafi ki tsaida ruwa (ruwan dai dai wanda zai dafa miki couscous naki zaki saka), Sai ki dauko maggi (iya dandanon da zai miki) ki sa kayan kamshi ki sa gishiri kadan, sai ki juya ki rufe tukunya ki barshi har sai ya tafaso.
 4. Dauko couscous na ki ki zuba a ciki sai ki juya. Sai ki dauko ganyen ugu, carrots, dafaffafen kwanki sai ki saka a saman couscous na ki sai ki kara yaryada yankakken albasa a ciki. Sannan ki dauko foil paper ko leda ki rufe saman couscous na ki sai ki kawo marfin tukunya ki rufe (amma ki rage wuta sosai) nadan wani lokaci.
 5. Daga karshe ki sauke ki sake juyawa (don su carrots na ki su hade da couscous na ki) sai ki zuba a plate.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here