Yadda ake miyar margi special

Win money on DrumbeatNews !!!

Yau a girke girkenmu za mu koyi miyar margi special. Za ku iya duba sabbin girke girkenmu kamar yadda ake tumki sauce da makamantan shi duk anan Bakandamiya.

 

Abubuwan hadawa

 

 • Danyen kifi
 • Stock fish
 • Cray fish (ki nika)
 • Alaiyaho
 • Yakuwa (ana sonta da dan dama)
 • Ganye ugu
 • Water leave
 • Albasa (ki yanka)
 • Tarugu da tattasai (ki jajjaga)
 • Maggi
 • Kayan kamshi
 • Man gyada
 • Daddawa (ki daka)

 

Yadda ake hadawa

 

 1. Za ki gyara stock fish na ki ki jika ko ki daura akan wuta nadan wani lokaci har sai ya yi laushi sai ki sauke ki raba shi da ruwan silalen ki ajiye a gefe. Sai ki dauko ganyen yakuwa da alaiyaho ki gyara ki wanke ki yanka su sai ki sake wankewa da gishiri ki tsane su a matsami sai ki ajiye a gefe.
 2. Dauko ganyen ugunki da na water leave ki hada su ki wanke ki yanka su sai ki sake wankewa da gishiri, ki ajiye a gefe. Ki yanka albasa dadan dama a wani kwano daban ki ajiye a gefe, su tarugu da tattasai a jajjaga su. Ki A ajiye a gefe.
 3. Sai ki dauko tukunya ki ajiye a akan table sai ki dauko ganyenki na su alaiyaho ki sa a farko. Sai ki dauko albasa ki yaryada akan ganyen. Sannan ki dauko tarugu ki sake yaryada akan albasan. Sai ki sa kifi ki jire akan tarugu, sai ki barbada kayan kamshi, daddawa, maggi (iya dandano da zai miki ), gishiri kadan, sai ki dauko stock fish ki sa akai, sai ki dauko ganyen ugu dana water leave (wanda ki ka gyara a baya) ki rufe kifinki dashi.
 4. Sai ki sake yaryada albasa, tarugu, da kuma Kayan kamshi kadan, maggi, daddawa dasu danyen kifin ki. Haka za ki yi ta yi har sai kin gama da ganyen da su kifinki sannan daga karshe ki dauko man gyada ki yaryada akai. Sai ki rufe tukunyanki ki daura akan wuta nadan wani lokaci (amma ki rage wuta , sosai za ki ga ruwa a hankali ya na fita a jikin ganyen) haka za ki barshi har sai ya nuna ruwan ciki ya shanye.
 5. Sai ki juya miyanki a hankali ki sauke sai ki zuba a plate. A ci dadi lafiya. Ana iya cin miyar margi special da tuwo shinkafa, eba, couscous da dai sauransu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here