Yadda ake coconut puff puff

Win money on DrumbeatNews !!!

 

 • Filawa kofi 1½
 • Kwakwa cokali biyu babba
 • Yeast cokali 1 babba
 • Madarar gari cokali biyu babba
 • Gishiri kadan
 • Suga cokali biyu babba
 • Ruwan dumi kofi daya

 

Yadda ake hadawa

 

 1. Ki gyara kwakwan ki cire dattin bayan sai ki gurza ta a jikin abun goge kubewa ki ajiye a gefe. Sannan ki dauko flour ki tankade a babban kwano madaidaici, sai ki dauko kwakwa ki sa a ciki flour, suga, madara, gishiri kadan, sai yeast ki sa (amma ki tabbatar yeast din mai kyau ne).
 2. Sai ki zuba ruwan dumi kofi daya a ciki sai ki kwaba kamar na minti 5 (ki tabbatar kwabinki ya kwabu sosai) sai ki rufe ki kai rana ya tashi kamar minti 20. Za kuma ki iya sawa a oven ba tare da kin kunna ba (zai tashi a hakanma).
 3. Bayan ya tashi ki dauko ki sake buga shi sosai kamar minti 2 sai ki daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai ki na diba ki na sawa ki na soyawa (amma ni nayi diban nawa kanana ne). Sai ki cire daga mai ki tsane shi.
 4. Daga karshe sai ki barbada sugar a kai (amma ba dole ba ne), shi kenan sai ci. A ci dadi lafiya.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here