Yadda ake coconut milk balls

Win money on DrumbeatNews !!!

Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke na Bakandamiya. A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake coconut milk balls ne. Amma kafinnan, mai karatu na iya duba girkinmu da muka koyar, a baya inda muka koyar da yadda ake sponge pancakes. To mai karatu ga yadda ake coconut balls dalla dallakamar haka:

Abubuwan hadawa

  1. Kwakwa (irin na leda ko kanti)
  2. Madara ta gari
  3. Condensed milk
  4. Sugar
  5. Chocolate
  6. Mai kadan

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko kwanonki babba, ki zuba madararki a ciki ki kawo kwakwa ki zuba sai ki sa condensed milk a ciki ki kawo mai kadan ki sa.
  2. Sai ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki shafa mai a tafin hannu ki, ki na diba kadan kadan ki na fadada shi ki na sa chocolate a tsakiyan kina mulmula shi har sai ya baki ball. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran kwabinki.
  3. daga karshe, sai ki barbada sugar a kai ki sa a fridge ya yi kamar minti 20, sai ki cire. Shi ke nan coconut milk balls na ki ya kammala.  A ci dadi lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here