Wani dan Bindiga ya kashe mutane 12 a yankin Virginia na kasar Amurka

Win money on DrumbeatNews !!!

A Virginia dake Amurka , daya daga cikin ma’aikatan da’irar garin dauke da bindiga ya bude wuta inda ya kuma kashe mutane 12, tareda raunata wasu can daban ,kafin daga bisali yan sanda su yi nasarar kashe shi.

Masu bincike sun bayyana cewa,maharin ya yita ruwan harsasai kan jama’a dake wurin da sama da mutane 400 ke zuwa a yankin na Vrginia.

Wanan dai ne karo na 150 da ake samun mutuwar mutane a kasar biyo bayan hari da bindiga kama daga farkon shekara ta 2019.

Kungiyoyi a kasar sun soma bayyana damuwa dangane da dokar malakar bindiga ,wacce aka jima ana tafka muhawara a kai.

Fadar shugaban kasar ta sanar da Shugaba Donald Trump halin da ake ciki yanzu haka,wanda ake kuma sa ran zai bayyana matsayin sa dangane da batun mallakar bindigogi da aka jima ana yi a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here