Tsohon Ministan Kudi Da Mutum Hudu Sun Fada Komar EFCC

Win money on DrumbeatNews !!!

Hukumar EFCC ta kai tsohon ministan kudi na lokacin mulkin PDP, Alhaji Bashir Yuguda Gusau, da Tsahon Gwamnan Jihar Zamfara a Jam’iyar PDP, Mamuda Aliyu Shinkafi zuwa kotu. Daga cikin wadanda aka gabatar a Babbar kotun Gwamnatin Tarayya ta Gusau, akwai shugaban Jam’iyar PDP na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Mallaha Gusau, Aminu Nahuce akan tuhumar su da karkatar da kudade bata hanyar da ta gabata ba. Mai gabatar da karar na Hukumar EFCC, Johnson Ojobane ne ya mika wa kotu tuhumar da ake wa tsohon Ministan da Mutum hudu akan karkatar da kudi naira biliyan Hudu da dari biyar ta hanyoyi daban-daban.

Wanda ya saba wa doka, maimakon su yi hulda ta banki sai su kayi ta hannu da hannu wanda wannan ya saba doka. A nan take bayan mai shigar da kara ya mika wa kotun tume-tuhume. Lauyan wadanda ake tuhuma, Jonh Charly  Shaka ya mika bukatarsa ga lauyan mai shigar da kara, na neman belin wadanda ya ke karewa. Lauyan hukumar EFCC ya ce kotu ce ke da hurumin bayar da beli, ba shi ba. A nan take kotu ta aminta da bada belin, akan sharuda goma sha daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here