Super Cup: Frank Lampard ya ce Chelsea ba kanwar lasa ba ce

Win money on DrumbeatNews !!!

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ce ya koyi darasi daga wasan da kungiyarsa ta buga a ranar Lahadi da Manchester, kuma ya nemi ‘yan wasansa da su nuna wa duniya ko su wane ne su a wasan Super Cup da za su buga da Liverpool.

Manchester United ta lallasa Chelsean bayan da suka kasa tare bayansu, inda aka tshi wasan 4-0 a Old Trafford.

Lampard ya ce, “Na amince da ‘yan wasana saboda haka bani da fargabar komai.”

Shi kuwa kocin Liverpool Jurgen Klopp na son ‘yan wasan kungiyar da “su cigaba da zama mayunwata” domin cinye wasu wasanni masu zuwa kamar na Super Cup.

Lampard ya kuma ce, “Dole ne dama mutum ya fuskanci kalubale a wasan kwallon kafa”. Yana magana ne a kan wasan na Lahadi.

Na san muhimmanci wannan wasan

Chelsea

Chelsea, who beat Arsenal to win the Europa League last season, are looking to win the Super Cup for only the second time.

Wannan ne karo na biyu a tarihin kungiyar ta Chelsea da take da damar cin kofin na Super Cup.

Sun doke Real Madrid da ci 1-0 a Monaco na kasar Faransa a 1998 inda suka daga kofin a karon farko.

Amma sun kasa maimata wannan kokarin a 2012 da kuma 2013.

Lampard na cikin ‘yan wasan Chelsea da suka kasa sake daukar kofin a wadannan shekaru biyun, kuma yana ganin: “Na san muhimmancin daukan wannan kofin ga Chelsea. Na san haka saboda da ni aka kasa daukan kofin har sau biyu.”

Sadio Mane, grappled by Jurgen Klopp, said he hadn't had a summer holiday for seven year

Klopp na son Liverpool ta “ci gaba da gashi”

A watan Yunin da ya gabata ne Liverpool ta lashe gasar Champions League a karo na shida bayan ta doke Tottenham 2-0.

Sannan kuma Liverpool ta lashe wannan kofin na Super Cup sau uku, wanda ya sa ita ce jagora tsakanin dukkan kungiyoyin kwallon kafa na Ingila.

Amma rabonsu da cin kofin tun 2005 inda suka yi bajintar nan da ta shiga tarihi bayan doke AC Milan wadda da farko ta ci Liverpool 3-0 kafin aka yi bugun daga kai sai gola bayan ta rama dukkan ci ukun.

An buga wasan na 2005 ne a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Kocin Liverpool Klopp ya ce, “Duk masu ganin Chelsea sun zama labule, to bani da abin da zan ce masu illa basu san kwallon kafa ba.”

Za buga wasan na lashe kambun Super Cup da karfe 8 agogon GMT na daren Laraba a birnin Istanbul.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here