Sojan sama ya mutu yayin basu horon diro wa daga jirgi

Win money on DrumbeatNews !!!

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da mutuwar wani jami’inta mai mukamain Corporal, Meshach Iliya Komo, yayin basu horon diro wa daga jirgin yaki. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da darektan yada labarai da hulda da jama’a, Daramola, ya fitar a yau, Lahadi. NAF ta mika sakon ta’aziyya ga iyalin marigayin bisa rashin jami’in sojin.

“Rundunar sojin na mai bakin cikin sanar da mutuwar daya daga cikin jami’anta, Corporal Meshach Iliya Komo, wanda ya mutu yau, 14 ga watan Afrilu, 2019, a Kaduna, bayan afkuwar hatsari yayin basu horon diro wa daga jirgi.

“A madadin rundunar sojin sama, shugaban rundunar, Air Marshal Sadique Abubakar, na mika sakon ta’aziyya ga iyalin marigayin bisa rashin da suka yi. Mu na masu addu’ar Allah ya ji kansa,” a cewar jawabin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here