Siriyawa miliyan 3.5 Turkiyya ke dauke da nauyinsu

Win money on DrumbeatNews !!!

Ministan harkokin wajen kasar Luxembourg Jean Asselborn ya bayyana cewar Siriya miliyan 3.5 da Turkiyya ke dauke da nauyinsu ba karamar nauyi bace

 

Ministan harkokin wajen kasar Luxembourg Jean Asselborn ya bayyana cewar Siriya miliyan 3.5 da Turkiyya ke dauke da nauyinsu ba karamar nauyi bace.

Asselborn ya yi sharhi akan tsarin ‘yan gudun hijiran Nahiyar Turai a yayinda yake hira da jaridar Osnabrücker Zeitung.

A cewarsa:

” Turkiyya na dauke da babban nauyi na Siriyawa miliyan 3.5. Dangane da haka akwai bukatar a bayar da tallafi. ya kara da cewa ya zama wajibi ga Tarayyar Nahiyar Turai da ta bayar da gudunmowa domin tallafawa Siriyawa dake Turkiyya”

Asselborn ya kara da cewa tallafin da za’a bayar za’a yi amfani dashi ne domin tallafawa Siriyawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here