Shugaban Faransa ya bukaci a cika wa G5 alkawari

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen duniya da suka yi alkawarin bada agajin kudi da kayan aiki ga rundunar Sojin G5 Sahel da ke yaki da ta’addanci a Mali da su gagaguta cika alkawarin su.

 

Shugaba Macron ya shaidawa manem labarai bayan ganawa da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issofou cewar babu abinda dakarun suke bukata cikin gaggauwa da ya wuce kudaden da rundunar za ta yi aiki da su.

Macron ya ce kudin da kungiyar kasashen Turai ta bayar anyi amfani da su wajen fara aikin rundunar, amma yanzu haka suna bukatar Karin kudade.

Shugaban Nijar Mahamadou Issofou ya ce suna bukatar gabatar da euro miliyan 420 da aka yi alkawari wajen gidauniyar taimakawa rundunar.

Issofou ya ce ya zuwa yanzu kasar Saudi Arabia ce kawai ta cika alkawarin ta na bada euro miliyan 100 wanda za’ayi amfani da su wajen sayen kayan aiki ga dakarun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here