Shabab na ta kashe Somaliyawa

Win money on DrumbeatNews !!!

Mutane 16 sun mutu,inda wasu sama da 20 kuma suka jikkata,sakamakon wata mota dankare da bama-bamai da ta fashe gaf wata cibiyar bincike ta ‘yan sandan sufuri da ke Mogadishu babban birnin kasar Somalia.

 

Shabab na ta kashe Somaliyawa

Mutane 16 sun mutu,inda wasu sama da 20 kuma suka jikkata,sakamakon wata mota dankare da bama-bamai da ta fashe gaf wata cibiyar bincike ta ‘yan sandan sufuri da ke Mogadishu ,babban birnin kasar Somalia.

A cewar bayanan da aka rawaito daga ma’aikatar jami’an ‘yan sanda ta kasar Somalia, motar mai cike makil da bama-bamai ta yi raga-raga a kofar wani gidan wasan kwaikwayo, a daidai lokacin da ta ke yunkurin kutsa kai cikin wasu shingayen da aka dasa a kan wata babbar hanya.

Bama-baman sun fashe a sa’ilin abar hawan ta ci karo da shingayen,inda nan take mutane 16 suka rasa rayukansu,wadanda a ciki har da magajin garin Mogadishu,Muhammed Abdullah Tulah, dan majalisar dokoki,Warsami Judah da kuma dan jarida,Awwal Tahir Saled,ma’aikacin tashar talabijin Universal TV,inda wasu mutane sama 20 kuma, wadanda yawancin su sojoji ne suka jikkata.

A gefe daya,an sake kai wani harin kunar bakin wake a babban sansanin sojojin birnin na Mogadashu,amma an tabbatar da cewa,babu wani wanda ya rasa ransa ko kuma jikkata.

Kungiyar ta’adda ta Al Shabab wacce ta yi kaurin suna a Somalia da kuma wasu kasashe makwabta ta fitar da sanawa,inda ta ce ita ce ke da alhalin kai wadannan munanan hare-haren.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here