“Saudia za ta tallafa wa Janar Haftar”

Win money on DrumbeatNews !!!

Shugabannin Masarautar Saudia sun yi wa janar Halifa Haftar,shugaban gambizar sojojin da ke iko da gabashin Libiya,alkawarin tallafa masa da milyoyinn dalolin Amurka a farmakan da yake ci aba da kaddamarwa da nufin  kwace iko da Trabulus.

 

“Saudia za ta tallafa wa Janar Haftar”

Shugabannin Masarautar Saudia sun yi wa janar Halifa Haftar,shugaban gambizar sojojin da ke iko da gabashin Libiya,alkawarin tallafa masa da milyoyinn dalolin Amurka a farmakan da yake ci aba da kaddamarwa da nufin kwace iko da Trabulus.

A cewar wannan labarin da jaridar Walla Street ta rawaito daga wasu manyan jiga-jigan masarautar Saudiyya, kwanakin kalilan gabanin ya fara kaddamar da farmakan kwace iko da Trabulus, Janar Haftar ya kai ziyara Saudiyya.

An tabbatar da cewa Saudiyya ta dau alkawarin tallafa wa Haftar da milyoyin daloli a gwagwarmyarsa ta kwace iko da Tarubulus.A wannan labarin, an kira mutumin da yau wannan alkawari da “Rumbun kundi,kowa ya same ka ya huta”,duk da dai ba a ambaci sunansa a karara ba.

A ziyarar da ya kai Saudiyya a ranar 27 ga watan Maris,Haftar ya gana da mai martabi sarkin haramaini,Sarkin Salman bin Abdulaziz da kuma dansa yarima mai jiran

A cewar kwamitin gwajin tsare-tsaren kakaba wa Libiya takunkuman makamai da Majalisar Dinkin Duniya ta samar,Haftar ya samu tallafin kasashen Ingila da na Masar.

Amma dai lokacin da gwamnatin Alkahira ke karyata wannan batun,kawo yanzu kasar Burtaniya ba ta ce uffan ba.

A cewar shugabannin kasar Amurka,Rasha ce ta bai wa Haftar tallafin kudi da na makaman yaki,amma an samu tabbaccin cewa gwamnatin Moscow ta ce wannan batun ba komai ba ne fa ce zuki ta malle.

Haftar da sojojin sun daura damarar kwace iko da Trabulus a ranar 4 ga watan Afrilun sehkarar 2019.

A wannan rikicin mutane 75 wadanda 7 daga cikin su faren hula ne sun rasa rayukansu,inda wasu 323 kuma suka jikkata.

Kasar Libiya dai ta kasa tsayawa kan kafafunta tun a shekarar 2011,inda rassa daban-daban na mayakan da ke kokarin kwace iko da kasar ke ci gaba yakar juna.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here