Sarkin Yarbawa ya bayyana wanda ya fi so tsakanin Buhari da Obasanjo

Win money on DrumbeatNews !!!

 

Sarkin Kasar Legas Rilwan Akiolu ya bayyana cewa ya fi sha’awar irin tsarin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a kan na tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo wanda yace Mayaudari ne kurum.

Oban na Legas Rilwan Akiolu a wajen wani taron bajakolin kasuwannin Duniya ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari zai gyara tattalin arzikin idan ya samu ya zarce. Sarkin yace Shugaba Buhari na da sauran aiki a gaban sa a Kasar.

Sarkin ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari mutum ne mai gaskiya ba irin Obasanjo ba wanda ya rika yaudarar Jama’a. Sarki Akiolu yake cewa idan Buhari ya samu lafiya ya zarce kuma ya samu nagratattu kusa da shi za a ga aiki.

Oba Akiolu ya bada labarin yadda su ka hadu da Buhari a 2011 da kuma 2015 lokacin ana ruwan sama. Sarkin yace a 2011 lokacin da Shugaba Buhari ya zo bai goya masa baya ba, amma a 2015 ya mara masa baya da su ka zo da Bola Tinubu.

Mai martaban ya nemi ayi wa tsarin tsaro garambawul domin yace ko da an canza hafsun Soji an yi aikin banza. Sarkin yace ya taba kallon Shugaba Buhari kwanakin baya ya fada masa illar soke aikin jirgin kasan Legas da yayi a 1984.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here