Rundunar ‘Yan Sanda ta Kashe Wani Shugaban Masu Garkuwa da Mutane a Edo

Win money on DrumbeatNews !!!

Rundunar ‘yan Sanda a jihar Edo a ranar Laraba ta Harbe wani Kasurgumin me Garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar, Johnson Kokumo, ya bayyana hakan wa manema labarai a Benin.

Kokumo yace jami’an rundunar ne suka harbe wanda ake zargin  a safiyar ranar laraba a yankin Ugbo dake jihar, bayan baza komar kamashi tun a ranar Talata.

Ya ce a ranar Talata, sun samu wani kira daga yankin cewa Shugaban kungiyar masu garkuwa da mutanen mai suna Mr Odion na a kofar gidansa.

Yace nan da nan ne rundunar ta tura kwararrun jami’anta don yin kwantan bauna a yankin da nufin kama jagoran masu garkuwa da mutanen.

Ya kara da da cewa a lokacin da wanda ake zargin ya fahimci jami’an na dakon shi, sai suka fara musayar wuta, inda ya kai ga kashe shi a nan take.

Kwamishinan ya ce wasu mutane guda Uku da ake zarginsu sun tsere amma suma an baza komar nemansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here