RONALDO – BANYIWA KOWA FADE BA.

Win money on DrumbeatNews !!!

Cristiano Ronaldo. Photo: 29 September 2018

Dan wasan kungiyar Juventus Cristiano Ronaldo ya musanta zargin da wata mata Ba’amurkiya ta yi masa cewa ya taba yi mata fyade a shekarar 2009.

Tsohon dan kwallon kungiyar Real Madrid din ya ce “labarin kanzon kurege ne.”

A wani faifan bidiyo a shafin Instagram, Ronaldo ya ce: “Suna so ne su tallata kansu ta hanyar amfani da sunana. Wannan abu ne da aka saba yi.”

Lauyoyin shahararren dan wasan sun ce za su yi karar mujallar kasar Jamus Der Spiegel wadda ta fara ruwaito labarin.

Mujallar ta ruwaito matar mai suna, Kathryn Mayorga, tana cewa shahararren dan wasan, mai shekara 33, ya yi mata fyade a wani otel da ke birnin Las Vegas na kasar Amurka.

Har ila yau mujallar ta ce Mis Mayorga, mai shekara 34, ta kai kara a wani ofishin ‘yan sanda da ke Las Vegas jim kadan bayan faruwar al’amarin.

A shekarar 2010, matar ta ce sun cimma yarjejeniyar wajen kotu da Ronaldo, inda ya amince zai biyata dala 375,000, idan ta ki bayyana wa duniya abiin da ya faru a tsakaninsu.

Sai dai a wata sanarwa da lauyan dan wasan Christian Schertz ya fitar ta ce: “labarin da mujallar Spiegel ta wallafa ya saba wa doka”.

Lauyan ya ce an umarce shi da ya nemi diyyar “bata suna” kan wannan ikirarin da mata take wa dan wasan.

Shahararren dan wasan ya koma kungiyar Juventus ne daga Real Madrid a bana a kan fam miliyan 99.2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here