RIKICI NA NEMAN BALLEWA DOMIN KASHE WANDA YA ZAGI ANNABI A PANDAGORI.

Win money on DrumbeatNews !!!

Wani shafi na facebook maio sunan Rariya ya kawo rohoton wani rikici da yake neman ballewa domin kashe wani mutum da akayi wanda yayi batanci ga Annabi.

Wannan ba shine fari ba akan irin wannan rikice rikice da suke aukuwa saboda batanci akan Allah ko annabi da wasu suke ma musulmai.

A koda yaushe dai wasu daga cikin musulmai suna yin yunkuri da kare addinin su ta kowace hanya. Duk da dai wannan kasa ce wacce ta ba yankasa damar da zasu furta dukan ra’ayinsu, wasu suna ganin amma bai kamata ayi amfani da daman nan don batawa wasu rayuka ba.

Koma me aka yima mutum, ya kamata ace ya kai kara ne a wajen hukuma. Daukan doka a hannu yana kawo damewar al’amurra da rikici da husuma.

Rariya sunce “Rikicin Na Neman Barkewa A Garin Pandogari Bayan An Kashe Mutumin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi (S.A.W)

Rahotanni daga garin Pandogari dake jihar Neja sun bayyana cewa yanzu haka rikici na neman ballewa a garin sakamakon kashe wani mabiyin addinin Kirista da aka yi sakamakon batancin da ya yi ga Annabi (S.A.W).

Majiyarmu ta rawaito mana cewa bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro sun yi ta kama mutane a yankin, wadanda akasarin su ba su da hannu a kisan da aka yi.

Sakamakon haka ne jama’a suka yi wa ofishin ‘yan sandan kawanya da nufin sai an saki mutanen da aka kama ko kuma su dauki mataki, kasancewar wadanda aka kama din ba su da masaniya kan kisan da aka yi.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ababen hawa ba sa zurga-zurga a yankin, sannan jama’a na shakkar fita harkokin su na yau da kullum don gudun ballewar rikici.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa RARIYA cewa suna bukatar a yada labarin domin shugabannin hukumomin kasar nan sun san halin da ake ciki a yanzu haka a garin na Pandogari, domin shawo kan lamarin tun kafin ya munana.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here