Rashin tausayi: An sace ta, an watsa mata ruwan guba

Win money on DrumbeatNews !!!

Fatima Habu Usman, daliba a Jami’ar Maiduguri wacce wasu bata gari suka sace ta da adaidaita sahu da tsakar rana sannan suka yi mata wanka da ruwan guba (acid).

Lamarin ya auku ne a ranar Juma’ar da ta gabata, a yayin da ta dauki shatar babur mai kafa ukun zuwa Baga dake jihar Borno, inda daga bisani suka jefar da ita.

Majiyar mu bata samu jin ta bakin hukumar ‘yan sanda dangane da afkuwar wannan lamari ba.

Kazalika bamu samu jin ta bakin fatima ba dangane da dalilin da ya kai ga har matasan sun yi mata wannan aika-aika.

Jihar Borno dai tayi kaurin suna wajen samun yawaitar tashe-tashen hankula daga kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here