2019: Bafarawa, Fayose Da Shema Sun Halarci Taron PDP A Katsina

Win money on DrumbeatNews !!!

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya shawarci magoya bayan Jam’iyyar PDP, da su dage da addu’a da kuma neman gafarar Ubangiji.

“Allah Yana horon ‘ya’yan Jam’iyyar ta PDP ne sabili da zunuban da suka aikata. “Allah Ba Ya yin kuskure, hakan ne ya sanya da ‘ya’yan Jam’iyyar PDP suka yi ma shi laifi, sai Ya karbe mulki daga hannun su ya baiwa APC, “ Bafarawa ya fadi hakan ne a wajen taron shiyya na Jam’iyyar ta PDP, ranar Asabar a Katsina. Shi ma Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ya nemi ‘yan Nijeriya ne da su guji aikata duk wani abu da zai iya karya tattalin arzikin kasarnan kamar na cin hanci da rashawa da makamantan hakan.

A na shi jawabin, tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya goyi bayan sake fasalin kasarnan ne, inda ya ce, hakan zai kawo ma kasar ci gaba a cikin hanzari. Ya ce, musamman sashen Bankunanmu da na siyasa suna bukatar sake masu fasali, domin karfafawa daukacin ‘yan kasa gwiwa su shiga a dama da su. Shema, ya karfafi ‘yan Nijeriya da su daina firgita da kiran da wasu masu nufin alheri ke yi na a sake fasalin kasarnan. A na shi takaitaccen jawabin, tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, shawartan magoya bayan PDP din ya yi da su manta da bambance-bambance su hada kai su yi aiki tare domin cin nasarar Jam’iyyar a zaben 2019.

Shugaban Jam’iyyar na kasa, Uche Sekondus, Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, Tsaffin gwamnoni, Sule Lamido, Ahmed Makarfi, Ramalan Yero, Ibrahim Shekarau da kuma Muntari Shagari da Aminu Wali, duk suna cikin manyan bakin da suka halarci taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here