Paul Biya: Ni da mulki mutu-ka-raba

Win money on DrumbeatNews !!!

A ranar Jummar nan da ta gabata,Paul Biya wanda ya share shekaru 35 kan karagar mulki,ya yanke shawarar sake tsayawa takara a karo na 7 a zaben shugaban kasar Kamaru da za a gudanar a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.

Paul Biya: Ni da mulki mutu-ka-raba

A ranar Jummar nan da ta gabata,Paul Biya wanda ya share shekaru 35 kan karagar mulki,ya yanke shawarar sake tsayawa takara a karo na 7 a zaben shugaban kasar Kamaru da za a gudanar a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.

Biya wanda ke ci gaba da jan akalar mulkin kasarsa tun a shekarar 1982,ya bayyana aniyarsa a washegarin wani hari da makami da ‘yan awaren yankin Kamaru wanda ke amfani da yaren Ingilishi suka kai wa ayarin motocin ministan tsaron gida.

Shugaban na Kamaru ya rubuta wani sako a shafinsa na sada zumunta na Twitter inda ya ce,”Zan zama shugaban kasarku a zabe mai zuwa.Kamata yayi mu hada kai don fuskantar matsalolin da Kamaru ke fama da su,tabbatar da zaman lafiya, bunkasa tattalin arziki da kuma kara karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin mu”.

Biya dai ya ce yanke shawarar zarcewa, don share kwallan ‘yan kasarsa na ciki da wajen Kamaru wadanda ke bukatar sake ganinsa kan karaga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here