Obama da matarsa Michelle sunfi kowa farin jini a duniya

Win money on DrumbeatNews !!!
An bayyana matar tsohon shugaban ƙasar Amurka Michelle Obama a matsayar wacce tafi ko wacce mace daraja da farin jini a duniya.

Kungiyar dake gudanar da bincike ta ƙasa da ƙasa wato Gallup ta bayyana cewar uwargidan tsohon shugaban ƙasar Amurka Michelle Obama tafi ko wacce macce farin jini, kambin da ta karɓe daga hannun tsohuwar ministan harkokin wajen Amurka Hillary Clinton wacce ta kwashe shekaru 17 tana riƙe dashi.
Hillary Clinton wacce ta kara da shugaban kasar Amurka Donald Trump ƙarƙashin jam’iyar Democrat ta kasance ta uku a jerin matan da sunka fi farin jini. Wacce tazo ta biyu ita ce Oprah Winfrey ma’aikaciyar wani gidan talabijin dake Amurka.
Daga cikin matan da sunka fi farin jinin goma akwai uwargidan shugaban Amurka Melania Trump da kuma sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ll.
Hukumar bincike ta Gallup da take gudanar da bincike akan farin jinin al’umma tun daga shekarar 1946 ta bayyana tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama a matsayin na ɗaya.
Bayan Barack Obama, shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, George W Bush, fafaroma Franciscus da kuma Bill Gates sun ka biyu shi a baya.
TRThausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here