Najeriya ta jinkirta kaddamar da kamfanin Nigeria Air.

Win money on DrumbeatNews !!!

Najeriya ta dakatar da shirinta na kafa kamfanin sufurin jrgin sama na gwamnatin kasar, ‘yan watanni kafin lokacin da aka shirya jiragen kamfanin za su fara aiki.
An dauki wannan matakin ne a yayin zaman majalisar zartarwar kasar na mako-mako a yau Laraba.
Wannan sanarwa ta dakatar da kafa kamfanin sufurin jiragen saman na Najeriya ta zo ne da bazata, ganin cewa kasa da wata uku ya rage wato a watan Disamba na wannan shekara da ake ciki ta 2018.
Gwamnatin ta sa lokacin da kamfanin zai fara aiki, ko kuma a ce jiragen kamfanin da za a kira Nigeria Air za su fara keta hazo.
Sanarwar ta bakatatan ta fito ne daga ministan sufurin jirgin sama na Najeriyar Hadi Sirika, ta wani sakon Twitter, a lokacin zaman majalisar zartarwar kasar, na wannan mako a yau Laraba.
Ministan ya ce, majalisar a yanzu ta jinginar da aikin kafa kamfanin sufurin jirgin sama na Najeriyar.
Duk da cewa ministan ya ce, dakatarwar ta wucin-gadi ce, amma kuma bai sanar da lokacin da za a dawo kan maganar ci gaba da aikin ganin jiragen kamfanin na Nigeria Air sun fara tashi ba, abin da ake ganin da wuya ya yiwu a nan da dan gajeren lokaci domin kasar na fuskantar manyan zabukanta a shekara mai zuwa.
A watan Yuli na wannan shekara ne daman gwamnatin Najeriyar ta kaddamar da suna da kuma tambari ko alamar sabon kamfanin sufurin jirgin saman nata a lokacin bikin baje koli na Farnborough Airshow a Landan.
Wanda dama ra’ayoyin ‘yan kasar ya bambanta game da aikin wanda aka ce zai lakume Naira miliyan dubu 1 da miliyan 200.
Wasu na ganin ya dace wasu kuma musamman masu hamayya da gwamnatin Shugaba Muhammnadu Buharin ta APC da cewa kamata yayin a yi amfani da makudan kudaden a wasu ayyukan raya kasa, kamar na lafiya da ilimi.
Gwamnatin Buharin dai ta yunkuro da niyyar kafa sabon kamfanin jragen saman na Najeriyar ne, wanda zai zama kusan a gurbin, tsohon kamfaninta na Nigeria Airways wanda ya daina aiki a shekara ta 2003.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here