Najeriya, Pakistan da Afghanistan ne suka saura da cutar shan-inna a duniya

Win money on DrumbeatNews !!!

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ta yi yara dubu 79 rigakafi a yunkurin da take yi domin kauda cutar Polio wato shan inna a Najeriya.

 

Najeriya, Pakistan da Afghanistan ne suka saura da cutar shan-inna a duniya

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ta yiwa yara dubu 79 rigakafi a yunkurin da take yi domin kauda cutar Polio wato shan inna a Najeriya.

Kodinetan cutar shan inna ta WHO a Najeriya Dkt Shola Ayeniyi ya shaidawa manema labarai da cewa a kamfen ɗin kauda cutar a halin yanzu anyi wa yara dubu 79 rigakafi.

Riga-kafinda aka kwashe kwanaki uku ana yi, Ayeniyi ya bayyana cewar kyauta ne kuma waɗanda aka baiwa maganin yara ne an ƙasa da shekaru biyar.

Ayeniyi ya ƙara da cewa ana ɗaukar matakai kwarara domin kauda kwayar cutar daga ƙasar baki daya.

A halin yanzu dai, a duniya ƙasashen Najeriya, Pakistan da Afghanistan ne ake samun bulluwar kwayar cutar shan innan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here