Nafisa Mohammad ta Bace a garin Abuja | Ana Rokon Jama’a dasu taimaka wajen Nemanta

Win money on DrumbeatNews !!!

Rahotan da muka samu na nuna cewa matar dake a jikin wannan Labari sunanta Nafisah Mohammad, wacce ke zama a titin Mashafa, Mpape – Abuja.

Ta bar gida a ranar Alhamis zuwa inda ba’a sani ba, ta bar diyarta mai shekara daya da rabi da haihuwa.

Makwafta ne suka sanar da mijinta ta hanyar kiransa a wayar hannu, bayan da suka rinka jiyo kukan yarinyar ba kakkautawa a daga cikin gidan.

Mijinta da ‘yan uwanta sun duba duk inda suke tunanin samunta amma basu sameta ba, sun kuma sanar da hukumar tsaro ta ‘yan sanda, asibitoci da kuma gidajen makwafta ko Allah yasa a sameta.

A halin yanzu mijin na cikin mawuyacin hali, kasancewar diyar tasu taki yarda ta zauna a hannun kowa inba shi ba.

Ya bayyana cewa babu wani sabani da ya shiga a tsakaninsu, bacewarta babban tashin hankaline a gareshi. Babbar matsalar kuwa itace babu wayar hannu a tare da ita.

Da hakane a ke rokon duk wanda Allah yasa ya ganta, ya tuntubi mijinta Tijjani akan lambobin waya 08065441791, 08155202396.

SHARE TO SAVE LIFE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here