Matan shugabannin Afrika sun bukaci kara haraji kan barasa da sigari

Win money on DrumbeatNews !!!

Matan shugabannin Afirka da ke halartar taron kungiyar kasashen nahiyar AU a Jamhuriyar Nijar, sun bukaci tsaurara haraji kan abubuwan da ke haddasa cutar Cancer, musamman taba sigari da kuma barasa.

Sika Kabore, uwargidan shugaban kasar Burkina Faso ce ta wakilci takwarorinta na sauran kasashen Afirka, wajen bayyana bukatar a ranar asabar.

Wani binciken masana yace akalla mutane miliyan 19 ke mutuwa duk shekara sakamakon kamuwa da cutar Cancer, kuma kashi 70 daga cikinsu a kasashe masu fama da talauci.

Matan shugabannin sun koka bisa yadda taba sigari da barasa ke da matukar saukin haraji da kuma farashi a nahiyar Afrika, sabanin yadda abin yake a Turai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here