Mata ta na yin zigidir kafin ta zageni, ba zan iya cigaba da zama da ita ba – Fasto ya fadawa kotu

Win money on DrumbeatNews !!!

Wani Fasto a cocin Pentecostal ya nemi wata kotu dake Igando a Legas ta raba aurensa da matar sa saboda tana amfani da al’aurar ta domin tsine masa.

A takardar da ya mikawa kotu, Fasto Bernard Towoju, ya shaidawa kotu cewar ba zai iya cigaba da zama da matar da za ta yi zigidir sannan take zagaya gidata tana ambaton al’aurar ta tana tsine masa ba.

Towoju, mai shekaru 53, ya ce masifar matar sa tayi yawa, har ta kai ga ya gaji da zuwa ofishin ‘yan sanda saboda yawan fadan da suke yi. A cewar Towoju, matar sa, Abosede, bata jin magana, ga rashin kunya da masifa kamar karya.

“Kullum sai munyi fada, mun yiwa juna rauni. Na gaji da zuwa ofishin ‘yan sanda, abin kunyar ya isheni haka. ina son kotu ta raba aurenmu,” a cewar Fasto Towoju.

KU KARANTA: Wata kungiya ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta fara binciken mulkin Obasanjo

Saidai da take magana a gaban kotun, Abosede, ta musanta zargin da mijin nata ke yi mata tare da shaidawa kotu cewar ‘yan tsibbu ke fadawa mijin cewar ita ce ta saka al’amuransa basa samun cigaba, dalilin da ya saka shi tsangwamar ta babu gaira, babu dalili.

Kazalika Abosede, mai shekaru 46, ta fadawa kotun cewar mijin nata ya gudu ya barta da dawainiyar yaransu har na tsawon shekaru goma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here